Malama Zinatu ta bayyana cewa, an boye wasu abubuwa na addini domin a batar da addinin na asali. Ta ce, masu irin wannan tunanin ne na batar da addini suka kai addinin a kasashe, an kuma dasa wannan tunani a zukatan musulmi kuma ta hanyar ilimi ne aka yada wannan,ta kara da cewa,karatu ne ya nuna wai shugaba ko azzalumi ne ,fasiki, dole ne abi shi. Ta ce , irin wadannan ne suka yi ma ‘yan mulkin mallaka dadi suka ba su damar mamaye kasashen musulmi, tare da basu damar raba siyasa da addini kuma wannan tunanin raba siyasar da addini ya somo asali ne daga mulkin banu Umayya.
Malama Zinatu ta kara da cewa, ‘yan mulkin mallaka na tunanin sun murkushe addini musulunci sai juyin Imam ya bayyana, kuma daga nan ne suka bullo da nuna bambancin Sunna Shi’a tare da cewa, Shi’a ba musulmi bane. Ta ci gaba da cewa, Imam ya gabatar da kiransa lokacin da sarki Sha ya dauki matakai na baza ‘yan leken asiri a ko’ina cikin kasar Iran, ya dasa tsoro a zukatan al’ummar kasar har a gida guda ba yarda da juna duk dai da nufin dakile bayyanar addinin na hakika. Ta ci gaba da bayyana cewa, har bayan cin nasarar Imam makiya sun ci gaba da shirya yadda za a rosa addinin tare da shan alwashin ba za su sake bari a samar da wata hukumar ta addini ba.
Da take bayyana darussa da za a iya koyo daga Imam,Malamar ta yi nuni da cewa ‘yanuwa su yi kokari su mallaki kaset na tarihin Imam mai suna ruhullah, su yawaiya kallonsa domin daukar darusa daga gwagwarmayar wannan bawan Allah. Idan ana ganin karanta rayuwar Manzo wani zamani ne mai nisa,to wannan abu ne da ya faru a wannan lokaci namu,sannan nasarorin da ya samu zaka ga cewa abu ne mai yiwuwa a wannan lokacin, sannan wannan tarihi na Imam za ya koyar da kai gwagwarmayar da Malam(H) yake kira zuwa gare ta.
Malama Zinatu , ta yi kira akan fadama juna gaskiya ta hanyar bayyana kusakuran juna domin a gyara. Ta ce farkon kiran nan abinda ya bambanta shi da saura shi ne wa azin da ke nunar da kai cewa da kai din ake, ba wazin da ke nuna kai ne na kwarai ba.”a rika wa azin da zaka ji koda kai baka aikata abu, maras kyau , amma zaka ji zoron aikatawa wata rana. irin wannan ya kamata a rika yi domin samun gyara.” ta bayyana muhimmancin sakonnin Malam su rika isa kunnuwan ‘yanuwa domin su fahinci hakikanin abinda Malam din yake cewa, domin abubuwa da dama suna faruwa kuma Malam ne yake bayyana mafita, kuma agane anan take ko kuma nan gaba.
Ta bayyna mamakin yadda yanuwa dalibai basu bukatar nuna kansu a matsayin masu addini cikin makarantu domin gudun tsangwama, ko kuma kora. Tace hatta wannan taro kamata ya yi ace a makaranta ne ake yinsa ba anan ba, ta nuna cewa idan ba a bayyana wa a makarantu yaushe wasu dalibai za su fahinta.
A karshe ta ce, ya kamata musan Imam Khomeine,mu dauki darasi daga rayuwarsa tare da aikata abubuwan da suka faru na darussa daga rayuwar sa,tare da yada wannan lamari ga al’umma, sannan t ace abi kyawawan tunani na Malam domin idan aka bi za a sami ci gaba, rashin nbin kuma ba Malam zaya cutar ba , mu da muka ki bi zamu cutu kuma mu yim asara.
A tun ranar farko da fara taron, Dakta Abdullahi ‘Yaradua ya gabatar da jawabi mai taken,Ilimi tushen gwagwarmayar tabbatatar addinin Musulunci , inda ya fara da cewa ilmi ya kasu kashi biyu ne.Ilmin Iyalan gidan Annabi da kuma ilimin da yake gaba da ilmin gidan Annabi. Ya kara da cewa, addini yana tabbata ne kawai idan an yi koyi da Iyalan gidan Annabi, ya kawo misalin yadda aka sami yunkure-yunkuren tabbatar addini a wasu kasashe, amma yunkurin ya ci tura saboda rashin yin koyi da Ilimin iyalan gidan Annabi. Ya bada misali da yunkurin ‘yan Ikhwanu na Misra, kungiyar FIS ta Aljeriya da kuma kungiyar Taliban ta Afaganistan. Dakta Abdullahi yatabbatar da wannan al’amari akan abinda ya faru a jamhuuriyar Musulunci ta Iran, inda ya nuna cewa,kasar ta samu nasara ne akan koyi da ilimin iyalan gidan Annabi da kuma dogara ga Allah (T) ya tabbatar da cewa, rikon kasar da iyalan gidan Annabi shi ya sanya ta gagari hatta makiya duk da cewa koyanshe suna kokarin ganin bayan kasar tun bayan juyin juya halin musulunci da aka aiwatar a shekarar 1979 a karkashin jagorancin marigayi Imam Khomenei (KS).
Dakta Abdullhi ya nuna cewa,ta hanyar koyi da wannan Ilim na Ahlul Baiti ne Allah ya buda kwakwalen al’ummar kasar da bangarorin Ilimi daban-daban ta fuskar Kimiyya , fasaha, tattalin arziki da sauransu, ya kara da cewa ita Iran bata yiwa Ilim tarnaki ba, wanda hakan ya basu damar ci gaba a bangaren fasahar iya kere-kere da hart akai su ga kera makaman da suke tada hankulan makiya. Sannan ya jaddada cewa, babu wani Ilimin da zaya iya tabbatar da Addini idan ba ya gangaro daga koyarwar ahlul baiti ba.
No comments:
Post a Comment