Wednesday, June 29, 2011

AN GABATAR DA RANAR SHAHIDAN GWAGWARMAYAR MUSULUNCI A ZARIYA

Kamar kowace shekara,  a bana ma harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(H), ta gabatar da taron ranar Shahidai  a karo na ashirin(20). a ranar Assabat 24 ga watan Rajab na wannan shekara ta 1432, a Zariya.
Kamar kowace shekara, Sayyid Zakzaky(H) shine babban bako mai jawabi, inda ya gabatar da jawabi da shafi bangarori da dama da suka hada da shahadar Imam Musa Al Kazim(AS) limamin shiriya na bakwai,Jawabi ga su shahidan harkar, sai nasiha ga 'iyalansu da 'ya'yansu gami da kira ga 'yanuwa da su tsayu wajen sauke hakkokin shahidai da ya doru a wuyansu da ya hada da ; Addu'a zuwa ga shahidan sannan bayar da hakkin Naira dari a kowane wata da ya doru a wuyan 'yanuwan,sai jawabi ga Azzaluman mahukunta da suke haifar da shahadar.

A jawabin na Sayyid ga Azzaluman, ya gargade su da su daina izgili ga addinin musulunci ta hanyar alakanta hare-haren bamabamai da suke faruwa a wannan kasa ga Musulunci da sunan Boko Haram,inda ya nuna cewa wannan ba abune da zaya kai su ga cimma manufofinsu ba na fada da addinin Musulunci,domin kuwa su Azzaluman ne da kansu suke kai wadannan hare-hare domin su cimma mugayen manufofinsu da suke da su a wannan kasa.
Ga kadan daga wasu hotuna da aka dauka yayin gbatar da wannan taro na tunawa da Shahidan gwagwarmayar Musulun ci a karkashin jagorancin na Sayyid Zakzaky(H) na wannan shekara:








 

No comments:

Post a Comment