A karo na tara,makarantar fudiyya ta Katsina ta gudanar da bikin yaye dalibanta da suka kamala karatunsu na primary a wannan shekara ta 1432, a ranmar Assabat 8/8/1432 a dakin taro na woman centre dake unguwar filin samji da ke Katsina.
A jawabin da ya gabatar,shugaban makarantar,Malam Kabir Sani, ya bayyana godiya ga Allah da ya nuna mana wannan lokaci, ya kara da cewa, manufar karatun primar da cewa, shine yaro ya iya karatu da rubutu, inda yace “muna godiya ga Allah da yasa yaranmu zasu iya kartantawa kuma zasu iya rubutawa sanna kuma suna da bakin gwargwado na masaniya akan addini.Da yake kokawa akan halin da kasa take ciki dangane da lalaceawar tarbiyya, sai yayimkira ga da’irar \yanuwa ta yankin Katsina da ta samar da makarantar gaba da primar don samar da kyakkyawar tarbiyya ga yaranmu gami da samun kyakkyawar fahimtar kiran komawa ga tafarkin Allah abinda yace ana samun rukushi a duk lokacin da yara suka bar makarantar fudiyya suka koma wasu makarantunsai ya yi fatan za a gaggauta warware wannan matsala domin cimma manufar da aka sa a gaba.
Ya kawo nasarorin da makarantar ta samu a wannan shekar da suka hada da samun nasarar fared a Zariya samun nasarar jarabawar science da har a wannan shekara ake sa ran samun nasararta ga kuma yunkurin da ake na fadada makarantar,sai ya yi kira ga iyaye das u kara sa kyakkyawar fahimta ga yadda ake gudanar da ayyukan makaranta ,su kuma rika binciken abinda ya shige masu duhu a inda ya dace dominkauce ma rudami
A jawabinsa Malam sabo ATC wanda shine shugaban lajnar fudiyya ta Katsinar ya jinjinawa malaman makarantar akan yadda suke iyakar kokarinsu wajen bayar da goyon baya ga shugaban makaranta abinda yak e kawo nasarorin da ake samu, sai ya yi kira ga ‘yanuwa baki daya da su bayar da goyon baya a kokarin da ake yi na fadada wannan makaranta,sannan ya tabbatar da cewa da yardar Allah za samar da makarantar gaba da primary domin rage matsalolin tarbiyya da ake cin karo dasu.
A jawabin da ya gabatar, Malam Jamilu Haruna Malumfashi wanda ya wakilci Malam Yakubu Yahaya a wajen wannan biki, ya bayyana cewa, Allah ya kawo mu wannan duniya ne fa domin mu bauta masa abinda baya yiwuwa sai da ilmi. Ya kara da cewa. Da yake haduwa ce ta ilimi ya yi kira ga daliban masu fita da su dage domin samun amfanin duniya da lahira, ya ce ya kamata amsar dalibin Fudiyyah ta zama fatan zama bawan Allah na kwarai, inda za a tambaye shi abinda yake so ya zama a nan gaba.
Ya karanto wasu halaye da suke taimakama mutum ya sami ilimi da suka hada da kyawawan dabi’u gaskiya , takatsantsan akan al’amurra rikon amana, Infaqi tsoron Allah da kulawa da salloli na wajibi da nafiloli gami da dakewa akan bautar Allah. Malamin ya yi bayani filla-filla akan wadannan dabi’u tare da karfafa su da ruwayoyi daga Limaman shiriya na gidan Annabi(AS) sai ya nuna takaicin yadda halayyar yanuwa take dangane da tsayuwa da sallolin nafila sannan ya nuna wajabcin kulawa da wannan bangare na salloli. Akarshe ya yi kira ga iyaye musamman Mata da su kara kulawa su kalli darussa daga rayuwar Sayyida Zahara(AS) na sauke nauyin tarbiyyar yara ta hanyar jawo su a jiki,sannan ya yi kira ga daliban da su yi karatu tukuru su dogara ga Allah kada su fada dabi’ar satar jarabawa da ta zama ruwan dare a halin yanzu ta yadda zaka ga dalibi baya iya kare takardar karatunsu
Ya yi fatan Allah ya kara taikamawa
An bayar da kyaututtuka ga dalibai masu fita da wasu daga cikin uwayen yara da suke taimakama makaranta da wasu kayan aiki, sannan aka bayar da wasu kyaututtuka ga dalibai masu kwazo na wannan shekara kana aka nada sabbin masu kula da ayyukan makaranta daga cikin dalibai watau prefects.
No comments:
Post a Comment