Friday, September 3, 2010

AN GUDANAR DA MUZAHARAR KUDUS A KATSINA

Daga Abdul Aziz

A ranar Juma’a 25/09/1431 wanda ya zo daidai da 3/09/2010 aka gudanar da muzaharar nuna goyon baya ga al’ummar Palastinawa da haramtaciyar Kasar Yahudawan Sahayoniyya ta Isra’ila suka kwashe shekaru kimanin sittin da uku ( 63) suna zalunta ta hanyar kisa , kamawa, rusa gidaje gami da killacewa.

Muzaharar wadda aka fara ta bayan kamala Sallar Juma’a, ta bi manyan titunan cikin garin Katsina da ta soma daga titin Mobil ta bi ta sabon layi, ta fice ta unguwar Kerau, sannan ta fito babban Asibitin Katsina ta dawo inda aka kammalata a bakin shatale-talen da ke bakin Masallacin Juma’a na cikin garin na Katsina.

Muzaharar wadda dandazon ‘Yanuwa Mazansu da Matansu suka fito daga sassa daban-daban na Da’irar ta Katsina da kewaye suna rera wakokin da ke bayar da sakon nuna goyon baya ga wadannan raunana da aka kwashe wadancan shekaru ana zalunta ta hanyoyi da dama.

A jawabin da ya gabatar bayan kamala wannan muzahara, Malam Yakubu Yahaya wanda akarkashin jagonacin sa aka gudanar da wannan muzahara, ya bayyana cewa,wajibi ne da ya hau kan dukkan al’ummar Musulmi su aiwatar da iri wannan jerin gwano domin kuwa duk lokacin da al’ummar Musulmi ta shiga wani hali, to wajibin sauran al’umma ne su nuna goyon bayansu. Sai ya yi nuni da cewa, irin wannan muzahara ana gudanar da ita ne a duk fadin Duniya baki daya domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu da aka share shekaru sittin da uku ana gallaza masu.

A wani bangare na jawabin Malam Yakubu ya dan tabo tarihin yadda aka kwaso Yahudawa aka jibge su a wannan wuri na Palastinawa, abin da ya bayyana da cewa dama kutungwila ce aka shirya. Ya yi nuni da yadda Yahudawan suke ‘yan tsiraru, amma sun addabi al’umma saboda yadda suka goge da munafunci da kulle-kulle sai yace, “ babu abinda ke maganin Yahudu illa addini” ya ce siyasa, yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya duk basu maganin Yahudu, saboda su mutane ne da suke bukatar zubar da jini musamman ma na Musulmi. Ya kara da cewa, duk wata yarjejeniya da za a shirya da su sai sun warware ta kamar yadda Allah ( T ) ya bayyana a cikin al’Qur’ani da cewa, “suna warware alkawali duk sa’adda aka yi shi” Sai ya yi nuni da cewa, duk wani zaman taro ko yarjejeniyar sulhu duk ana yinsa ne a ISKA. Sai ya ce maganin wannan shine “idan Yahudu suna da akidar mamaya da zubar da jinni; to su kuma Musulmi suna da akidar shahada da shiga Aljanna” wannan kuma shine maganin Yahudu sannan kuma wannan abu ne mai yiwuwa domin an gwada a baya a lokacin da ‘yan Ikhwanu na Misra suka fafata da yahudawa abin da ya sa aka kulla makircin kama Mujahidai, ya ce, amma a yanzu Allah ya sake ta do wasu mujahidan irinsu Hizbullahi da Hamas ga kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadanda kullum a shirye suke su yi maganin Yahudawan.

Sannan ya yi nuni da cewa, irin wannan muzahara da ake yi tana da tasiri, domin yanzu suna ganin duk duniya tana kware masu baya ne. sai ya yi kira da cewa kada mutum ya ga irin wannan tarurruka da ake yi wani abu ne na sha’awa ko marmari, a’a yana da makasudi kuma Allah yana isar da wannan makasudi. Saboda ana yi ne domin Allah da kuma amsa kiran Manzon Allah da ya ce,” wanda ya ji wani Musulmi yana neman taimako amma bai taimake shi ba , to shi ba Musulmi ba ne”sai ya ce wannan yana daga cikin irin gudunmuwar da muke iya bayarwa. Ya yi fatan Allah ya nuna mana kaskantar wadannan Yahudawa.

No comments:

Post a Comment