DAGA: ABDUL'AZIZI
Da Yammacin ranar Juma'a ne 02/10/1431 ,Da'irar'yanuwa Musulmi almajiran Sayyid Ibarahim Zakzaky(H) ta Katsina da kewaye ta shirya tare da gabatar da wa'azin goron Sallah a babban masallacin Juma'a na cikin garin Katsina,a karkashin jagorancin Malam Yakubu Yahaya .
A jawabin da ya gabatar Malam Yakubu ya bayyana cewa,
“Shugabanni ke fada da mu, ba mu ke fada da shugabanni ba"
Malam Yakubu ya ci gaba da cewa abinda muka sani Mu bayin Allah ne, kuma mun san cewa Allah ya raba shugabanni zuwa gida biyu, masu shiryatarwa da umurnin Allah horo da kyakkyawa da hani ga mummuna da kuma masu kira zuwa ga shedan. Kuma wannan shine abinda Allah ya tsara” Ya ce kuma wannan shine abinda Sayyid Zakzaky(H) ya kwashe sama da shekaru 30 ya na kira zuwa ga reshi cewa, ba za a bi shugabancin masu kira zuwa ga bata ba " Mu ba fada muke da shugabanni ba su ma ne ke yin fada da mu” domin ba mu yarda da bin shugabani masu kira zuwa ga bata ba, wannan shine ma matsalar idan ma akwai matsala, domin suma shugabannin dole ne akansu su bi Allah (T). sai ya kara da cewa, lokacin boye-boye akan bayyana addini ya wuce idan dai har mabarnata za su dinga shelanta wannan barna tasu a kafofin yada labarai a Duniya, to kamata yayi musulmi su yayata addininsu. Malam Yakubu Ya nuna takaicin jin yadda Malamai a wannan wata na Azumi suka yi ta yayata ayi addu'a ga wadanna shuwagabanni masu jagorantar mutane bada littafin Allah ba. Ya ci gaba da bayyana cewa, wasu suna cewa ai wannan kasace mai addinai kamar kuma yadda yake a tsarin mulkinta, amma kuma Allah shi cewa ya yi, "addini a wurinsa shine musulunci" sai ya yi tambayar cewa, yaya zaka yi ka gamsar da Allah(T) idan kace ka yarda da cewa kasa ce mai addinai ga shi kuma Allah ya ce "wanda duk ya riki wani addini ba musulunci ba, ba a karba masa ba kuma a Lahira yana cikin tababbu'.Tunda Allah ya ce haka, to kai kuma tsammaninka Allah ya yarda da tsarin da ake tafiya akansa da jagorancin da ake da shi a wannan kasa?
Malam Yakubu ya ci gaba da bayyana cewa, wasu suna ganin addini a matsayin ci baya wanda kuma aka ga yana rike da addinin ana ganinsa cibayayye, a ganin masu wannan ra'ayi, rayuwar Turawa ita ce cigaba da kuma wayewa.Sai ya kawo misalin irin wadannan kasashe da ake ganin sun ci gaba da cewa, a halin yanzu saboda tabarbarewr atarbiyya, gami da aikata munanan laifuka har dokar ta baci ake sawa a wasu kasashen domin maganin aikata muggan laifuka. Sai ya ce, addini ne kadai zai yi maganin irin wadannan matsaloli.
Da ya tabo irin yadda al'umma ke kauce ma wahalhalu akan kin bin tafarkin addini ,sai ya ce, Allah ya halicci mutum ne a cikin wahala ba domin jin dadi ba a wannan duniya' Allah ne kuma ya tsara ma dan Adam irin wahalar da za ya sha daga cikin wahalar kuma har da akwai jihadi da Ibada wadda cikinta har da Azumi wanda aka kammala, shi ma yana daga cikin irin wannan wahala, yace kuma shi wannan Azumi Allah ya sanya daga cikin hikimominsa har da gyara halayen mutum, domin shi mutum yana da wasu halaye munana kamar fushi, sha'awa da sauransu wadanda idan mutum yana yin Azumin, to za ya daidata masa wadanna halaye ta hanyar tsoron Allah da zaya samu. Sai ya nuna wajabcin yin addini domin shine za ya gyara dan Adam.Malam Yakubu ya kawo irin yadda Annabawan Allah suka yi tsayin daka wajen fuskantar wadannan wahalhalu haka ma Mujaddadai domin dai kawai a tseratar da dan Adam daga shiga azaba a Lahira, sai ya yi kira ga Malamai da su fada ma jama'a gaskiya.
A tun farko sai da Malam Yakubu ya bayyana yadda wannan wa'azi na goron Sallah ya samo a sali a wajen 'yanuwa a wannan gari, inda ya ce , tun farko lokacin 'yanuwa ba su da yawa ,idan irin wannan lokaci ya zo , akan kai ma juna ziyara ne saboda neman ladar dake akwai ga yin ziyarar, daga baya da aka kara yawaita ya zamo ba za a iya zuwa gidajen junaba , sai aka fara gabatar da shi a wannan muhalli, ganin kuma yadda jama'a ke lekowa sai aka rika nasihantar Juna domin samun amfanuwa.
A karshe ya yi fatan Allah ya kawo ma wannan al'umma mafita daga wannan mawuyacin hali da ake ciki.
Malam Yakubu Yahaya Katsina a lokacin da aka gabatar da goron Sallah
No comments:
Post a Comment