Daga:AbdulHamid Ilya Ganuwa,
08162234919 / 08125661551
Taro, ya yi taro! Ba shakka taron da Makarantar Fudiyya Rijiyar Lemu ta kira a
garin Kano, a madadin Da’irar Kano don bikin taya murna ga daliban da Allah Ya horewa haddace littafi mai girma,watau Alkur’ani mai tsarki, wadda aka gabatar a garin Kano, ranar Lahadi 4 ga watan Shawwal ya yi nasara.
Babbar nasarar da taron ya samu, itace halartar babban Bako, Shehu, Mujaddadi, Sayyid Malam Ibraheem Ya’aqub Zakzaky (H) wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana kiran al’ummar Musulmin kasar nan da a koma wa bin tsarin Allah Ta’alah, watau bin dokokin Allah da ke cikin Alkur’ani mai girma.
Wannan gagarumin taro da aka gabatar a bi sa jagoranci da kuma kulawar mai masaukin baki, Wakilin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a birnin Kano, Malam Muhammad Mahmud Turi, ya samu halartar Sayyid Malam Ibraheem Zakzaky (H) tare da Amirorin `yan uwa na garuruwa da kauyuka da ke sassan kasar nan.
Haka ma taron ya samu halartar manyan bakin da aka gayyata a cikin birnin Kano da wasu sauran garuruwa a wannan kasa. Kadan daga cikin bakin da suka samu halartar taron sun hada da, Shugaban Mahaddata Alkur’ani mai girma na Kano, Shugaban Shariffai na Kano, Alarammomi Mahaddata kuma Marubuta Alkur’ani mai girma, Limaman Masallatan Juma’a da sauran dimbin bakin da ban iya kiyaye sunayensu ba.
Dubban `yan uwa Musulmi almajiran Sayyid, Malam Ibraheem Zakzaky (H) na cikin birnin Kano da sauran garuruwa da kauyukan Kasar nan maza da mata, manya, yara da tsofaffi da `yan uwa na Jamhuriyyar Kasar Nijar sun samu halartar wannan taro na taya daliban Fudiyya Rijiyar Lemu murnar samun nasarar hardace Alkur’ani mai girma.
Wannan taron taya yara murnar haddace Alkur’ani mai girma ya samu gagarumar hidima ta kai-kawo, shirye-shiye da tsare-tsare da abin da ka-je-ya-dawo a bisa kulawar dakarun Harka Islamiyya, watau Hurras.
Suma `yan ISMA, watau masu kula da lafiyar al’umma a Harka Islamiyya, sun bayar da tasu gudumuwar sosai a wajen kulawa da marasa lafiya a yayin gudanar da taron.
Haka suma Sha’irai, watau Mawaka Harka Islamiyya sun jiyar tare da dadadawa mahalarta wannan gagarumin taro baitocin wakoki masu dadin gaske kafin fara taron da kuma bayan gama jawabin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
Masu aikawa kafafen watsa labaru da rahotonni, da aka fi sani da `yan Jarida da masu daukar hotuna, suma sun samu halartar wannan kasaitaccen biki na taya yara murnar haddace Alkur’ani mai girma da aka yi a birnin na Kano.
A filin taron dai an samu tsara rumfuna kamar haka, Rumfar Babban Bako Sayyid Malam Ibraheem Zakzaky (H). A kwai kuma Rumfar Manyan Baki da aka gayyata.
A kwai kuma Rumfar `yan uwa mata, watau sisters, Rumfar Sharifai, Rumafar Alarammomi, Rumfar Limaman Juma’a, Rumfar `yan Jarida, Rumfar `yan ISMA, Rumfar almajiran Sayyid Zakzaky (H) da suka fito daga wasu garuruwan kasar nan da Kauyuka da kuma Rumfar yara maza da mata Mahardata Alkur’ani mai girma da dai sauran rumfuna masu yawa.
A can bayan filin taron kuwa `yan tijara (`yan kasuwa) ne suka baje kayayyakin sayarwa iri-iri, kala daban-daban don masu bukata. A waje daya kuma masu sayar da abinci ne da masu sayar da ruwa ga wadanda Allah Ya ba ikon halartar wannan taro da aka yi a wannan rana ta lahadi.
Kadan daga cikin manyan matsalolin da na lura da afkuwarsu a wannan taro mai muhimmancin gaske sune, rashin isar masu tsara wajen taron da wuri, wanda hakan ya kawo kurewar lokaci a yayin taron, musamman takaitaccen lokacin da Sayyid ya amfana da shi ya yin ya gabatar da jawabi.
Sai kuma matsalar kayan sauti, musamman lokacin da ake gabatar da yaran da aka shirya taron don taya su murnar haddace Alku’ani mai girma sadda ake gabatar da su ga mahalarta taron a ya yin da suke karanta Ayoyin Alkur’ani mai girma, wanda ba’a samu jin karatun na su a wurin taron sosai ba.
Sannan kuma rashin jin sautin ya jawo daruruwan mahalarta taron da ke can baya wadanda muka samu zantawa da su, sun shaida mana cewa ba su ji jawabin da Sayyid Zakzaky (H) ya yi ba, kasancewar sauti bai kai wa in da suke. Da fatan Allah Ya bamu ikon gyarawa.