Gatancin da zaka yi ma danka shi ne ka ba shi ilimi,
musamman ma na addini.Malam Yakubu Yahaya ya bayyana haka a yayin kaddamar da makarantar hardar alkur’ani mai girma da
Da’irar ‘yanuwa Musulmi almajiran Sayyid Ibrahim ZakzakY(H) yankin Katsina ta gabatar
a ranar 20 / 11/ 1433 a matsugunnin makarantar na gajeren lokaci da ke tsohuwar
Markaz dake Unguwar vyari a cikin birnin Katsina.
A farkon jawabin nasa, Malam Yakubu ya tabo kadan daga cikin
tarihin yadda aka fara gabatar da karatun harder al’Qur’ani tun daga lokacin
Sahabban Manzon Allah, a lokacin da suka fahinci cewa, mahardatan al’Qur’ani
suna karanta sakamakon Shahada da wasunsu suka yi a fagen fama.
Malam Yakubu ya ci gaba da bayyana cewa, al’Qur’ani shi ne
jogon tafiya a wnnan harka ta Musulunci, shi ne kuma zaya gyara al’umma kamar
yadda ya gyara al’ummomin baya.Ya tabo yadda turawa suka sami ci gaba sakamakon
shiga kaashen musulmi da suka yi suka karanto ilmomi da malaman musulunci suka
rubuta sakamakon karantar al’Qur’ani, sai ya nuni da cdewa da Bature bai zo ya yi
mana barna ba, da yanzu mun kai wani matsayi na ci gaba.sai ya bayyana cewa, za
a karantar da al’Qur’ani da manufar samar da ilimomi da fannoni daban-daban
domin samar dam asana da suka san duniya kuma suka san Lahira.Ya ce,” za a
koyar da duk wani fanni na ilimi, wannan shi ne gurinmu”
A wani sashen jawabin nasa,Malam Yakubu ya ankrar da dukkan
‘yanuwa cewa, kasancewar wannan makaranta ta fara ne a mazauni na gajeren
lokaci kafin samar da mazaunin tan a dindindin, akwai bukatar ‘yanuwa su san da
cewa, akwai aikin samar da wannan mazauni sannan kuma ga shirin samar da
makarantar Sakandare ta Fudiyya da shi ma ake yunkurin yi domin samar da
ingantaccen ilimi ga ‘ya’yanmu.Saai ya gode ma wadanda aka dora ma nauyin ganin
an fara wannan karatu sannan ya bukaci iyaye das u koma makaranta domin gyara
ma yaransu duk wani nkuskure da zasu yi a lokacin da suke bita a gida, domin
wanda baida abu ba zaya iya bayar da shi ba.
A karshe, Malam Yakubu ya nasihanci malaman wannan makaranta
da yin hakuri da matsalolin da zasu iya fuskanta a yayin tafiyar da harkokin
wannan makaranta.
A zantawar da almizan ta yi das hi, shugaban Lajnar
makarantar ta Tahfizul Qur’ni, malam Shehu karkarku, ya bayyana cewa samar da
wannan makaranta aiwatar da irshadin da sayyid Ibrahim Zakzaky(H) ne ya yi a
shekaru biyu da suka gabata a kano yayin saukar karatu da aka gabatar, inda ya
bukaci kowane yanki ya samar da irin wannan makaranta.
An kammalam wannan taro na kaddamarwa ta hanyar yanke zare
da Malam Yakubu ya yi ,sannan ya fara karantar da yaran a matsayin fara karatu
a wannan sashe na harder littafin Allah mai girma.