Sunday, June 10, 2012

ACADAMIC FORUM YANKIN KATSINA YA GABATAR DA TARON MAKON IMAM KHUMEINE(KS) NA WANNAN SHEKARA TA 2012



Aranar Lahadi 10/ 6/ 2012 , dandalin dalibai na Acadamic Forum yankin Katsina ya gabatar da taron tunawa da makon Imam khomene (KS) na wannan shekara a dakin taro na ‘women centre’ dake unguwar  filin samji Katsina.

A jawabin da ya gabatar, Shekh Muhammad Mahmud Turi, wakilin Sayyid  Ibrahim Yakubu Zakzaky(H) a birnin Kano , ya karanto kadan daga tarihin Marigayi Imam Khumene(KS). Malam Turi ya bayyayana cewa, Imam ya  taso ne a gidan Ilimi, amma a yanayi na maraici domin mahaifansa sun rasu tun yana karami,amma a haka ya yi  ta rayuwa irin ta neman ilimi ya kuma rayu a cikin yanayi  karancin abin hannu domin an tabbatar da cewa, a lokacin bargo daya ne kadai ya mallaka, amma a haka ya ci gaba da neman ilimin.Malamin ya  ce, tun yana da kananaan shekaru ya fara koyarwa a Hauza saboda hazaka da Allah (T) ya  ba shi.Malam Turi ya kara bayyana cewa, Allah madaukakin Sarki ya haska ma  Imam halin da al’ummar iran ta ke ciki na rashin bin dokokin Allah, bayan da Imam ya fara wayar ma al’umma da kai sai gwamnatin Sha, ta yi yunkurin kashe shi, abinda ya sa Malamai suka bayyana Imam khomene a matsayin Ayatul lahi, hakan yasa dole Sarki Sha ya janye yunkurin kasha shi, sai dai gwamnatin ta kore shi daga Iran ,inda ya yi hijira zuwa kasar turkiya sannan daga can zuwa kasar iraki, inda a can din ma dai ya ci gaba da wayar ma al’umma kai musamman abin da ya shafi Fikira akan ‘Wilayatul fakihi’ watau jagorancin Malami, wannan kira na imam ya jawo masa kyama daga Malamai.
malam Turi ya kara da cewa, duk lokacin da Musulmi suka yi watsi da tsarin Allah, to rayuwarsu zata kasance a cikin kaskanci, kamar abinda yake faruwa a wannan kasa a halin yanzu. Ya ce, Imam ya ci gaba da kokarin wayar ma mutane kai akan  hadarin bin tsarin gwamnatin da bata musulunci ba domin rashinta gwamnatin musulunci na hana aikatuwar musuluncin. Malam Turi ya kara da cewa, Imam ya yi gwagwarmaya da malamai fiye da yadda ya yi da Kafirai, domoin Malaman suna zarginsa da kawo cikas wajen bayyanar Imam Mahadi(AJ)
Malam Turi ya bayyana wasu darussa da za a dauka a rayuwar wannan bawan Allah inda malamin ya yi tambayar cewa, Mi yasa Imam ya sami wannan nasara , amma ga dimbin Malamai basu sami wannan ba? Sai ya bada amsar cewa, Imam ya na da zuciya daya,sai ya ba Allah(T) wannan zuciya sai Alah ya hore masa zukatan al’umma.  

Malam Turi ya kirayi ‘yanuwa akan yaki da zukata  domin kauce ma abubuwan da za su bata zuciya saboda shagaltar da ita tare da  gurbata ta yadda ba zata iya yunkurin gwagwarmayar  tabbatar da addini ba.
A lokacin da yake kira akan kulawa da tarbiyyar ‘ya’ya, Malam Turi ya bayyana cewa, gurin makiyanmu shi ne  su bata tarbiyyar  musulmi, sai ya bayyana muhimmancin kulawa da  tarbiyyar yara domin su kasance sun sami tarbiyyar addini domin su zamo cikin rundunar da zata zamo ta Allah. Da zata taimakama addini.
A wani bangaren jawabin nasa, ya bayyana cewa, duk jama’ar da tadanfaru da Imam Khomenei, za a ga bambanci da sauran  koda kuwa Shi’a mutum ya ke yi.Ya bada misalin wasu kasahe irin su Pakistan da suke da Shi’a, amma saboda basu damfare da Imam basu sami daukaka ba, amma ga Hizbullahi nan yadda suka buwaya.
A karshe ya bayyana cewa, a wannan kasa babu mafita ga al’umma sai ta hannun Mujaddadin wannan al’umma  Sayyid Zakzaky(H) kamar yadda shehu Usman dan Fodiyo ya  yi bushara.’abinda ya kamace mu shi ne riko da wannan gwagwarmaya ta hanyar kyautata alaka da Allah kamar yadda Sayyid Zakzaky(H) ya ke kira akai’

Saturday, June 2, 2012

DANDALIN MATASA NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA YANKIN KATSINA YA GABATAR DA MAULUDIN FATIMA(AS) A GARIN KANKIA, JIHAR KATSINA


Zama matashi mai addini babban matsayi  ne, kuma falala ce daga Allah(T). Malam Yakubu Yahaya ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabin mauludin Syyida Azzahara(AS) da dandalin matasan harkar musulunci karkashin jagorancin Sayyid  Zakzaky(H) na yankin da’irar Katsina da kewaye ya shirya ya kuma  gabatar a dakin taro  na ‘Shema youth empowerment  Centre’ dake garin Kankia, jihar Katsina, a ranar Lahadi  7 /7/1433.

Malam Yakubu  ya ci gaba da cewa, duniya gaba dayanta, a wannan lokaci matasa ne suke tafiyar da ita, ina ya bada misali da manyan kasashen  duniya  dama wannan kasa da cewa,shugabanninsu duk matasa ne, haka idan aka dubi rundunonin soji  da sauran jami’an  tsaro na duniya, duk za a ga dai matasa ne  suke jagorantar su, ya ce, duk wasu bangarorin tafiyar da al’amurran al’umma dai zaka ga cewa,matasane ke rike da su. Ya ce, hakama  lamarin Lahira ta matasance,inda  ya bayyana Imam Hasan da Husaini (AS) a matsayin shugabannin aljanna. ya kuma karanto kissar Annabawan Allah da suka hada da Annabi Ibrahim da sauransu da irin gwagwarmayarsu da zalunci duk suna matsayin matsa ne suka aiwsatar da haka. Sannan  idan aka dubi ashabul  Kahfi  suma matasanne,ya ce, wadanda suka rufa ma Manzo baya a lokacin kiransa irinsu Imam Ali ,Sayyida Zahara(AS)  da sauran su  ,za a ga cewa dai matasan ne.ya kara da cewa, haka ma Mujaddadai  irinsu Shehu dan Fodiyu Da Imam Khomenei (KS) duk matasa ne suka dafa masu sai ya ce duk wannan yana nuna maka cewa,matasa sune  jari na duniya da Lahira, kuma akan yarinta ake gina duniya da Lahira,ya kara bayyana cewa, “ba girman jiki bane , zuciya ce mai kyau da ta  siffantu da ibada.” sai  ya ankarar da matasa akan yunkurin da makiya suke yi na  rosa tarbiyyarsusannan ya   nuna wajabcin lura tare  da kauce ma afkawa cikin hadartin wannan tarko. Sai ya bayyana mafita daga wannan tarko da cewa, itace addini ,”a dasa ma matashi tsoron Allah, ibada da son  Lahira tare da tsaron azabarta ,”kuma wannan shi ne manufar kiran Sayyid  Zakzaky(H) ,  ba  al’amarin neman mukamin duniya ba ne”,
Ta bangaren Sayyida Zahara(AS) kuwa, Malam Yakubu ya tabo wasu kadan daga matsayai  da falalolin da Allah ya bata Musamman Tsayuwarta dadagewarta akan bin Allah da taimaka ma sakon da aka aiko Manzo  Da shi,sannan ya bayyana  cewa, al’amarin ahlul Bayt abu ne  mai hatsari domin kuwa abu ne wanda ya shafi Imani.Ya kara da cewa,zaka ga mutum ya yi imani da sakon Manzo a dunkule , amma  da an ce ayi dalla-dalla sai ka ga yana shafa keya bai yarda ba. Ya tabo abubuwa da dama  da suka shafi  hakkkin ahlul Bayt da suka hada da Khumusi,Wila’a  da jagorancin su  kamar maganar  ‘ Halifofi bayana Sha biyu ne” kamar  yadda yake a littafan Buhari da MUsulimu, amma dai mutane  ba su yarda ba, inda zaka ga babban Malami idan aka yi masa wannan bayani baya yarda, haka kuma yake ga sauran musulmin duniya. Sai ya yi mamakin yadda kiriri aka maida Halifofin Annabi  guda Hudu, bayan shi Annabin ya ce Sha biyu ne kamar yadda ya zo a Buhari da Muslim,  ya ce “lallai akwai hadari akan wannan” ya kammala da cewa, ” Ba so bane kawai, a‘a  bi ne ga wadannan  bayin Allah”