Tuesday, May 15, 2012

MUZAHARAR MAULUDIN SAYYIDA FATIMA AZZAHARA (AS) A KATSINA




‘yayanuwa mata almajiran Sayyid Ibarahim Zakzaky(H) dake  da’irar  Katsina, sun shirya  tare da gabatar da  muzaharar  mauludin Sayyida  Fatima azzhara diyar Manzon Allah (S) ta wannan shekara a wannan rana ta Talata,24/6/  1433 
.
Muzaharar  wadda  aka soma da misalin karfe tara da rabi na safiyar  wannan  rana , ta sami halartar ‘yanuwa  mata  daga yankuna  daban-daban na cikin garin Katsina  da kewaye, a  bisa      rakiyar Harisawa  da  suke a goshin wannan muzahara , sannan ‘yan makarantun Islamiyyu na ciki da wajen garin  Katsina da suke dauke da tutoci iri daban-daban  ana tafe mawakan Harkar musulunci na rero baitocin  yabo ga Sayyida Fatima(AS)  dama wakokin mahaifin ta da sauran “ya’yanta  A’immatul huda(AS).
Muzaharar  wadda  ta zagaye  muhimman  titunan garin Katsina, ta kayatar ainun ida aka kwatanta ta da wadanda suka gabace ta, duk da karacin abubuwa kamar yadda daya daga cikin masu shirya ta  ta shaida ma  manema  labarai da suka zanta da ita. Malam Bilkisu idris  ta ce, “akwai shirye-shirye da  za a gabatar idan Allah ya nuna mana ta shekara mai zuwa, wanda ta ce, za su fadada shirin domin gayyato mata daga bangarori da yawa na cikin garin Katsina.
A jawabin da ta gabatar bayan kammala wannan muzahar, Malama Safiya Kabir, ta bayyana  wasu kadan daga cikin matsayai  na wannan  baiwar Allah da cewa, ita  ce wadda Allah da kansa ya daura mata aure da babban bawansa Imam Ali (AS), sannan ta bayyana takaicin irin wahalhalu da wannan baiwar Allah ta hadu da su tun bayan wafatin mahaifinta  Annabi  Muhammad (S).Ta ce, a yunkurin rufe matsayi  da darajarta  ne,  ba za ka taba jin ana karanto wasu Hadisai da za a danganta ruwayarsu daga wajen ta ba, domin  kada jama’a  su fahinci wasicin da Annabi ya yi  na bain  shiriya a hannun jikokinta, sai tayi  fatan al’umma  musamman ‘yanuwa  mata  za su yi bita akan rayuwarta su kuma yi koyi da halaye irin na Fadima(AS).
Kafin wannan muzahar, sai da kwamitin ‘yanuwan mata ya gabatar da wata ziyara zuwa ga malaman makarantun  allo dake yankuna  hudu na bangarorin da ake da su  a wannan  da’ira  da suka hada da yankunan  Gabas, Yamma, Kudu da kuma Arewa  wtau  (Zones) tare da gabatar ma almajirai da malamansu  kyaututtuka  na  abinci  da kuma sabulan wanki albarkacin wannan baiwar Allah .
Za dai aci gaba da gabatr da wannan gagarumin biki na tuna haifuwar diyar Manzon Allah Fatima azzhara (AS)  a rana daya da ta rage  inda Malam Yakubu Yahaya zaya gabatar da jawabin karshe na wannan biki.


Sunday, May 6, 2012

A KARO NA UKU: AN TUNA DA SHAHADAR ALHAJI IBRAHIM HAMDALA CHARANCI


A karo na uku, Mu’assasatus shuhada  da   bangaren ‘yanuwa na kwamitin ahl-duthour  yankin da’irar Katsina, suka gabatar da taron tunawa da shahadar  Alhaji Ibrahim  hamdala  Charanci  dake  jihar  Katsina  da yammacin ranar Assabat 14/6/1433.
 A jawabin da ya gabatar, Malam  Shehu  Dalhatu  Karkarku, ya bayyana Shahada  da cewa falala  ce da Allah (T) yake  bayar da ita ga daidaikun bayinsa musamman a irin wannan lokaci da al’umma bata  bisa tsarin  Allah. Malam Shehu Dalhatu ya bayyana matakai  da Shehu Usmanu  Mujaddadi  ya  bayyana da suka wajaba musulmi su dauka  a duk lokacin  da suka  sami  kansu a wurin da ba  a bin dokokin Allah, wadannan  abubuwa  kuwa  sune, kauracewa  daga wannan wuri  da ya  bijire  ma tsarin  Allah, ko kuma gwagwarmayar  tabbatar  da tsarin  Allah din  ko  kuma mutum  ya tafi daji ya sami wata itaciya ya ciza har sai ya mutu.
Ya yi tir da  yadda  ake  ta yunkurin  bata  kiran komawa  ga tsarin Allah  da sukar kiran da sunan ana shi’a, wai kuma shi’ar  ba addini ba ne. Yace, “amma kiran shi ne mafita ga al’umma  daga wannan yanayi  na zalunci da ake ciki” daga nan Malam Shehu ya gutsuro matsayin shahidi da bayyana kadan daga  cikin matsayan da suka hada da , ceton mutane  saba’in  daga cikin danginsa,  bayan  rahama da yake  cikinta  tun kafin tashin kiyama. Ga makasan Alhaji Ibrahim kuwa,  ya bayyana matsayinsu ne na dawwama cikin azabar wuta  kamar yadda Allah(T) ya fada a cikin littafinsa mai tsarki.
A tun farko sai da aka gabatar da ziyarar Shahidin a makwancinsa, inda Malam Muhammad Awwal  Iyal Zariya  ya gabatar da takaitaccen jawabin da a cikinsa ya tunatar akan irin ta’addancin da aka yi ma Alhaji Ibrahim  na kisan gilla ba domin komi ba  sai dai saboda imaninsa. Ya  kawo misalin halin da al’umma take  ciki na zalunci da kashe-kashe  da ake ta yi  akan musulmi, inda ya bayyana mafita daga wannan yanayi  sa cewa, ita ce, matsayar da Imamu Husaini(AS) ya dauka a lokacin da ya ga addinin Manzon Allah  yana fuskantar  rusawa, abinda ya kai ga shahadarsa .malam Awwal ya kara da cewa, gwagwarmaya a irin wannan lokaci ita ce kawai mafita, ya yi nuni da cewa, ko a kasashe irin su Iraki da  Amerika  ta kai mamaya  tana kashe  jama’ar  kasar, g wagwarmaya  suka yi  har sai da Amurka din ta ga babu wurin zama sannan ta fara janye sojojinta  daga kasar. Sai ya ce a wannan  kasar ma gwagwarmaya  karkashin jagorancin  Sayyid Zakzaky(H) tare  da  tsayuwa  akan tafarki  ne  kadai zaya kawo  mafita ma wannan al’umma .
Idan za a iya tunawa, kimanin shekaru uku  da suka gabata ne,  wasu  gungun ‘yan ta’adda  suka kai ma shahid  Alhaji  Ibarahim Hamdala hari a gidansa bayan ya tashi daga shagonsa, inda suka sassare shi har suka shahadantar da shi.
‘Yanuwa daga garuruwa da dama  ne suka sami halartar wannan tunawa  da shahadar  tasa.