Friday, November 26, 2010

YADDA DA'IRAR KATSINA TA GABATAR DA IDIL GADEER A SHEKARAR 1431

Daga: Abdulazizi / Zaharadden
                                                                        
                
A ranar Juma'a 20 ga watan Zul-Hijja  1431 Hijiriyyah, wanda ya zo daidai da 26 / 11/ 2010 Miladiyyah, Da'irar 'yanuwa Musulmi almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky(H) ta katsina ta gabatar da taron wa'azin murnar Idil Gadeer na wannan Shekara ta 1431, a harabar masallacin Juma'a dake cikin birnin Katsina.
Taron wanda ya fara da misalin karfe hudu da rabi na yammacin ranar ta Juma'a, an bude shi ne da karanto wasu daga cikin ayoyin al-Qur'ani mai tsarki da ga bakin dan uwa Malam Adamu Gobarau. Bayan sa ne sai Malam Sabo ATC ya gabatar da 'yan wasan kwaikwayo na Dan Fodiyo, inda Malam Ahmad Kofar Sauri ya jagoranci gabatar da 'yanwasan, inda suka gabatar da wata Tamsiliyya mai kayatarwa mai suna "CIN AMANA". tamsiliyyar ta yi nuni ne da abubuwan da suka faru a tarihi na canja wakilcin da Manzon Allah (SAWW) ya yi, tare da kawo wasu abubuwa da suka shafi hana Sayyida  Zahara(AS) gadonta gami da zuwa gidanta da aka yi aka banka kyauren da ya yi sanadiyyar zubewar cikin da take dauke da shi Na Muhsin da kuma yin sanadiyyar Shahadarta daga bisani. Masu gabatar da tammsiliyyar sun yi kokarin isar da sakon nasu cikin hikima tare da sakaya sunayen duk masu hannu a afkar da wannan waki'a.

Daga nan ne sai aka ba mawakan gwagwarmaya dama suma suka bada tasu gudunmuwa ta hanyar wake Imam Ali Zakin Allah.(AS).
Wanda ya gabatar da jawabi a wannan taro shi ne Malam Shehu Usman Dalhatu  Karkarku a madadin Malam Yakubu Yahaya. Mal Shehu ya bayyana cewa Wannan Munasaba ta Gadeer ,Munasaba ce da ta shafi dukkan Musulmi ba 'yan shi'a ba. Munasaba ce wadda Manzon Allah ya kama hanun ImamAli(AS) ya daga sama, sannan ya ce "wanda na kasance Shugabansa, to ga Ali nan shine Shugabansa" san ya yi Addu'a da cewa"Allah ka taimaki wanda ya taimake shi, ka kuma watsar da wanda ya watsar da shi" . Sanna sai ya jawo hankalin Musulmi da cewa, wannan al'amari ba siyasa bace kamar yadda wasu suke gani, a'a addini ne. Malamin ya ce ,ko da yake bayan Manzon ya yi wafati,wasu sun sun canja sun zabi na su shugaba. Saannan sai ya yi tambaya ga masu ganin 'yan shi'a basu yarda da wannan canji ba da wasu suka yi akan na Manzo da cewa, wasu Sahabban suma  basu yi bai'a ba ga wannan canji, su ya ya zaka ce masu?
da ya juya kan yadda aka kirkiro Hadisai na karya, irin masu nuna cewa' wai Manzo ya ce" abi shugaba, na kirki ne ko  fajiri" sai ya ce irin wadannan Hadisai ne suka sa musulmi suke bin Fajiran shugabanni abinda ya kai su ga bin jagorancin kafirin Shugaba. Sannan yace " idan ka damfara jagorancinka ga wanda ba Manzo ne ya ayyana shi ba, to bai yi daidai ba"

Sannan ya jawo hankalin al'umma da cewa Manzo ya yi umurnin Duk wanda ya ji wannan sako , ya isar da shi ga  wanda bai ji ba, Uba ya isar ma da 'ya'yansa, 
A karshe ya bayyana cewa, idan har addini ba shi da jagoranci iriin wanda Manzo ya kafa, to dole ne za a ci gaba da zama cikin rigingimu, kuima idan ka rasa jagorancin Imam Ali (AS) zaka ci gaba da zama karklashin jagorancin Fajirai.
 Ya yi fatan Allah (T) ya amsa mana wannan Wila'a da  muka yi ga Imam Ali (AS) a karkashin jagorancin Sayyeed Zakzaky(H).


Wani bangare na 'yanuwa suna sauraren jawabin da Malam Shehu Karkarku ya gabatar a wajen taron Gadeer da Da'irar Katsina ta gabatarta


'Yanuwa mata suna sauraren jawabin Gadeer da aka gabatar a Katsina

                                                                                        


Monday, November 15, 2010

LAJNAR ISLAMIYYU KARKASHIN HARKAR MUSULUNCI TA GABATAR DA ADDU'AR KWANA ARBA'IN DA RASUWAR MALAM ISHAQ RAFIN DADI

Daga: AbdulAzizi

Lajnar Madarisil Islamiyyah tahti Harakatil Islamiyya ta da'irar Katsina ta shirya tare da gudanar da tunawa da kwana arb'in da rasuwar Malam Ishaq Rafin dadi Katsina da yammacin ranar Talata 3/ 12/ 1431.

Da yake gabatar da takaitaccen jawabi a gaban kabarin Malam Ishaq, Malam Shehu Dalhatu Karkarku wanda ya wakilci Malam Yakubu Yahaya wakilin 'yanuwa almajiran Malam Zakzaky(H) na Katsina, ya fara ne da gabatar da sakon Malam yakubu, inda ya ce,"Malam Yakubu din yana jaddada ta'aziyyarsa ga 'ya'ya , 'yanuwa da almajiran Malam Ishaq gami da mika wannan ta'ziyya ga 'yanuwa almajiran Malam Zakzaky(H) dangane da wannan babban rashi da mukayi" Malam Shehu wanda ya bayyana cewa Malam Yakubu ya yi gurin ya kasance da shi ne ake gabatar da wannan tunawa da rasauwar wannan bawan Allah ,amma saboda kasantuwar ya yi tafiya bai sami damar kasancewa a wannan muhalli ba.

Malam Shehu Ya bayyana cewa Hakika Allah ya karbi rayuwar Malam Ishaq a daidai lokacin da al'umma ke da bukatuwa zuwa ga shiryarwarsa wanda ya dake akan gaskiya duk da tsangwama da yayi ta fuskanta, amma ya dake har Allah ya tabbatar da dugadugansa kamar yadda muka gani. Malam Shehu ya ce, ba shi kadai yake kwance a wannan wuri ba,amma ga shi Allah ya taro masa zukatan Muminai masu kuka dangane da rasa shi, suka baro wuraren ayyukansu suka kawo masa wannan ziyara ta kwana arba'in domin tunawa duk dai albarkacin kiran da Malam din yake yi duk dawannan tsangwama da ya hadu da ita domin raya al'amarin Addini.Sai ya bayyna wannan rasuwa ta Malam Ishaq da cewa, :tunatarwa ce, "ya rage ga remu da muka saura " sai ya yi kira ga 'yanuwa da su yi shiri domin fuskantar wannan rana ta mutuwa.

Malam Shehu ya kuma yi kira ga Malamai na wannan gari, da su yi koyi da Marigayi Malam Ishaq ta hanyar hada kan almajiransa da sauran Musulmi ba kokarin raba kan su ba.

Malam Abubakar Kofar Durbi wanda ya wakilci Shugaban Lajnar Malam yakubu Idris , ya bayyana cewa makasudin shirya wannan tunawa da rasuwar Malam Ishaq, shine domin tabbatar da zumuncin dake tsakanin Malam da 'yuanuwa. ya bayyana cewa shirya wannan munasaba, an yi ta ne bisa umurnin Malam Yakubu Yahaya wanda ya karfafa akan gabatar da ita domin a hadu a bayyana ayyukan wannan bawan Allah . Ya kara da cewa, an gayyato 'yanuwa 'ya'ya da almajiran Malam Ishaq ne ga mi da shirya wasu addu'o'i da karatun al'Qur'ani mai tsarki tare da gabatar da jawabai da babban dansa da kuma almajirinsa hada da Wakilin Malam Yakubu Yahaya zasu gabatar da daren na wannan rana ta Talata domin a bayyana ma jama'a irin gudun muwar da yake bayarwa wajen amsa kiran hadin kan musulmi da Malam Zakaky(H ) yake jagoranta a wannan nahiya., musamman ganin shi kadai ne wanda ya yi fice wajen karba kiran hadin kai da ake yi duk lokacin Mauludin Annabi(SAW) a duk shekara.

A Jawaban da aka gabatar da dare, Manyan almajiran Marigayi Malam Ishaq suka gabatar da jawabai a takaice kan yanda Malam din ya yi kokarin ganin ya koyar da su al'amurra na addini da dama, ciki kuwa har da nuna kauna ga Manzon Allah wanda dama shine abinda Malam Ishaq ya yi fice aka kuma sanshi akan haka.

Malam Ishaq ya yi fice wajen karba kiran makon hadin kai da harkar musulunci ki gabatarwa a duk shekara, shine Malami kwara daya da baya tsoron nuna goyon bayansa ga kiran Malam Duk da cecekucen da yake gamnuwa da shi a tsakanin Malaman garin Katsina akan yadda yake gwamatsar almajiran Malam Zakzaky(H). Taron kareshe da ya halarta na makon hadin kai da Da'irar Katsina ta shirya a mauludin da ya gabata , ya nuna a wajen cewa, babu wani abin da zaya hana shi halartar taron nuna mauludin Manzon Allah, gami da sauran jawabai da ya yi masu matukar gamsarwa da sallamawa ga kiran Malam(H).

Malam Ishaq ya rasu a yanayin da duk wani mumini yake fatan ya yi irin wannan rasuwa, ya rasu a daren Juma'a kuma yana kalmar shahada tare da girmama Allha madaukakin sarki.

Al'ummar da suka hadu wajen wannan zikira duk sun kasance cikin wani yanayi na damuwa da juyayin tunawa da wannan bawan Allah. An yi addu'o'in fatan Allah ta'ala ya tabbatar da kyakkyawan fatan da Muminai suke yi akan sa, da fatan kara gabatar masa da karin adduar nema kasancewa tare da Manzon Allah(SAW) wanda Malamin ya yi suna waje gaba da duk wanda ya kuskura ya yi sakin baki a kan Mauludin haifuwarsa.