Saturday, December 22, 2012

AN BUDE BANGAREN ISLAMIYYA NA MAKARANTAR FUDIYYAH KATSINA



A ranar Laraba 6/2/1434 ne aka  bude bangaren karatun Islamiyya a makarantar Fudiyya dake Katsina.
Da yake gabatar da jawabi a wajen bikin,Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na garin Katsina, ya bayyana godiya ga Allah (T) ne Daya bada wannan dama da aka samu na koyar da yara wannan addini wanda shi ne makasudin zowar dan Adam a wannan duniya, kamar yadda Allah (T) ya fada a littafinsa mai tsarki.ya ce ,sai ka san addini ne zaka  san abinda zaka iya saka ma jikinka,sai ya bayyana ilimi da cewa, ba karamin al’amari ba ne,inda ya nuna cewa, duk abinda yak e a wannan duniya , ilimi ne ya samar da shi,sannan ya kara da cewa, sabo da muhimmancinsa ne ,Allah ya umurci Manzonsa da ya roki Karin ilim, kamar yadda ya zo a littafin mai tsarki na al-Qur’ani.Sai ya yi kira da cewa,  bai kamata a bar mu a baya ba a wannan fage.
Malam Yakubu ya kara da cewa, tozarta addini ne ya haifar mana da matsalolin  da muke ciki,inda ya nuna takaicin yadda ake gudanar da al’amarin addini, ya bada misalin yadda al’umma take gabatar da ayyukan bauta  ba bisa ka’idar addinin ba. Kamar gabatar da Sallar magariba tun kafin faduwar rana ta shari’a, da sauran misalai da suka shafi karatun al-Qur’ani mai girma. Ya kawo misalai da dama dangane da haruffan Larabci da yadda suke bambanta da na Hausawa inda ya ce kusan yawanci Bahaushe yana gabatar da karatun sallar sa  da haruffan Hausa ne a madadin na Larabci, sai ya nuna wajabcin mu gyara wadannan matsaloli. Sannan  kuma Malam Yakubun ya yi kira da mu kawo yaranmu su koya yadda ya kamata.Sai ya bayyana kulen da al’ummar  musulmi suke fuskanta  na yunkurin dakile lamurransu na addini da iliminsu ta hanyar bullo da makirce-makirce a kowane lokaci ga kuma kulen gyara tsakanin mu da Mahalicci ta hanyar yin addininmu yadda yake.
Karshe ,malam Yakubu ya kira ga iyaye da su dage su tura yaransu a makaranta neman ilimi sanna suma iyayen su koma makarantar domin gyara abinda ya kubuce masu.
A tun farko. Shugaban makarantar Fudiyyah Malam Kabir Sani , ya bayyana makasudin bude wana bangare ne da cewa, domin ba yaranmu ilimin addini ganin cewa a makarantun book ba a ba ilimin Musulunci muhimmanci ba, sannan kuma a ba yaran kyakkyawar tarbiyya ta addini.

                                      

Sunday, December 9, 2012

AN KAMMALA ZAMAN MAKOKIN SHAHADAR IMAM HUSAINI(AS) A KATSINA


A ranar Talatar da ta gabata ne, aka kawo karshen zaman makokin Shahadar Imam Husaini(AS) wanda Da’irar ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) taKatsina ta shirya kuma wakilin ‘yanuwan Da’irar ta Katsina Malam Yakubu Yahaya ya kwashe kimanin kwana ashirin yana gabatarwa.
A wannan karatu na zaman makokin Imam Husaini(AS), Malam Yakubu ya kawo Dalilai da suka jawo wannan waki’a ta ashura, inda ya karanto daga cikin littattafan Ahlussunati, abubuwan da suka faru tun daga lokacin da Manzon Allah ya riski Rahamar Mahaliccinsa, inda ya karanto abubuwan da suka shafi warware bai’a ta hanyar canza nadi tare da zaben halifanci sabanin wanda Manzon Allah ya yi.
Bayan karantar yadda waki’ar ta Ashura ta faru, an kuma karanto abubuwa marasa dadin ji da addini ya gamu da su bayan kisan gillar da aka yi ma Imam Husaini(AS) kamar kisan Sahabbai da ruguza garin Madinar Manzon, yakar Makka tare da rusa Ka’aba ta hanyar jifar ta da majaujawa da rundunar Yazidu ta yi.
Bayan kammala karatun ne , aka yi addu’ar neman samun damar daukar fansar wannan ta’addanci da makiya Allah suka yi wai kuma da sunan su Musulmi ne. Sannan malam Yakubun ya yi kira ga musulmi da su karanci wannan addini na musulunci ta hakikanin koyarwar gidan Annabi, tun da dai wannan addinin Annabi Muhammad ne aka aiko da shi, kuma koyarwarsa tana nan tare da Iyalan gidansa.