Alhaji Abdullahi Abubakar (khairan) wanda ya yi magana da yawun ISMA a lokacin wannan ziyara, ya yi wannan kira a yayin zantawa da wakilinmu a harabar asibitin a ranar Juma'a 25/3/ 2011. Alhaji Abdullahi ya bayyana cewa, ganin yadda wannan yajin aiki yake barazana ga jama'a musamman kasancewar babu wata asibiti komin kankantar ta indai ta gwamnati ce, to wannan yaji aiki ya shafe ta, abin da ya jawo cikewar asibitocin kudi dama daya ta gwamnatin tarayya dake akwai a jihar.ya kuma yi kira ga kungiyoyin sakai da ke bayar a agaji a asibitin da su kara hakuri da wannan yanayi mai ban tausayi. sannan ya bukaci Sauran 'yanuwa da suke bayar da gudunmuwar kudade da su kara sadaukarwa domin kuwa al'amarin yana bukatar jurewa ganin babu wani shiri na dakatar da yajin aikin. Ya nuna godiya ga kungiyar abokan asibiti akan tallfawa da suke yi da kudade domin samar da magunguna da ake rabama jama'a marasa lafiya kyuta.
Ya yi godiya ga Allah da ya taimaki 'yanuwan da sadaukarwa sabo da Allah kamar yadda Sayyid Zakzaky(H) ya koyar da su.
Ya bayyana cewa kimanin sama da Naira dubu sittin(60,000) suka shige wajen sayen magunguna daga ranar da hukumomin asibitin suka gayyaci 'yan ISMA din a ranar Talata 15/3/2011 zuwa yau, ya yi nuni da cewa, ba a san yawan marasa lafiyar da zasu iso asibitin ba sakamakon labarin Yanuwan na ISMA suna bada taimako a asibitin, ya zuwa yanzu kimanin mutane dubu daya da dari uku da talatin da biyar (1335)ne suka je neman kulawa tun daga fara yajin aikin.
Kungiyoyi da dama ne suke bayar da gudunmuwa a asibitin dalili wannan yajin aiki. tare da 'yan ISMA ,kungiyoyin da suka hada da jam'atu nasril Islam, Yan agaji na Izala ,hizba , Boy scout.
Idan za a iya tunawa, a cikin watan Azumin Ramadan ne ma'aikatan kiwon lafiyar suka gudanar da makamancin wnnan yajin aiki domin neman wasu bukatu da a lokacin aka yi yarjejeniyar za a basu a cikin watan Janairun wannan shekara, to amma dai har yanzu ba a basu wadannan kudi ba, kamar yadda wata majiyar ta nuna.
Jama'a dai da dama suna sa albarka da addu'ar fatan alkhairi ga almajiran na Sayyid Zakzaky(H) saboda wannan gudun muwa da suke bayarwa.
'yan ISMA a bakin aiki