Sunday, April 22, 2012

MU'ASSASATUS SHUAHADA'U TA GABATAR DA TARON KARA MA JUNA SANI NA WUNI UKU A KATSINA







A karo na biyar, Mu’assasatus Shuhada’u a Harkar musulunci a  Najeriya  da Sayyid Ibrahim Zazaky(H)     yake yi ma jagoranci, ta shirya taron karama juna sani  na ‘ya’yan Shahidan Harkar wanda yankin Shahid Hamza da ke KAtsina  ya shirya  a  garin  tun daga ranar Juma’a  29/5/ ha r  zuwa 1/6/ 1433.
A jawaban da  aka gabatar da suka kunshi muhadarori da masu jawabai . Dokta Abdullahi  Dan Ladi wanda ya yi jawabi aklan ‘ Ilimi ginshikin rayuwa” ya  bayyana  ilimin  da cewa, haske ne da Allah yake jefa shi a cikin zuciyar wanda ya ga dama, inda  ya  bayyana cewa, kowace halitta da Allah ya samar, to tana da nata ilimi da aka kimsa mata sai dai ilimin yakan bambanta  da na  juna. Dokta Abdullahi  ya bayar da misalai akan halittu na dabbobi da yadda suke rayuwa a tsakaninsu  abisa  ilimi  da Allah  ya hore masu, sai  ya  ce  amma ilimi dan  Adam ya bambanta dana dabba.
Dangane da ilimin Dan Adam,  cewa  ya yi,akwai wanda  mutum  ya  gada  kuma  yake koyo acikin al’uimmar da yake rayuwa  a cikinta sannan wanda ake koyowa a hannun malamai.
Dokta  ya  bayyana cewa, rayuwar mutum bata takaita anan duniya ba, akwai wata rayuwar ta bayan mutuwa, sai  ya ce, duk  wanda aka halitta , to za a yi masa Hisabi, kuma  ana  yi ma mutum  Hisabinne gwargwadon Iliminsa , ya bayyana  cewa, sai mutum  ya san Mahaliccinsa  sannan ne zaya iya bauta masa yadda ya kamata, sannan dole aikin mutum ya tafi kafada da kafada da iliminsa. Sai ya bayyana ilimin boko da cewa da shi da na addini duk daya ne matukar dai mutum ya yi  ilimin  domin Allah  da kuma niyyar taimakama al’umma. Ya kara da cewa, kamar yadda za a iya yi ma mutum azaba akan ilimin boko, to haka ma za a iya yin azabar ga mai ilimin addini madamar mai na  addini  bai yi amfani da ilimin  ba. Sai ya bayyana al’amarin karatu da cewa, ba abune mai sauki ba sai an dage sannan ne ake samunsa. Sai ya bukaci ‘ya’yan Shahidan da su  dage su kokarta su taka duk wani fage na ilimi da ake da shi, kuma a shirye Mu’assasar  take ta dauki  nauyin duk dan Shahidin da ya sami damar kara karatu kowane iri ne .
A jawabin da ya gabatar  Malam Abdull Hamid Bello Shugaban wannan Mu’assasa ta Shahidan Harkar musulunci, ya yi Magana ne akan kyawawan dabi’u, inda ya karanto Hadisai masu dama da suke Magana akan matsayin dabvi’u masu kyawu. Malam Abdul Hamid ya bayyana  tarbiyya   da cewa, ita ce,yin aiki mai kyau da barin maras kyau” Sannan ya bayyana cewa, Allah ya aiko mana da abin koyi watau Manzon Allah (S) wanda yake rahama a cikin halittu,sannan wannan Manzo shine madubi  da zamu kalla domin koyon dabi’u  daga wajen sa.Sai ya bukaci mahalarta da su siffantu da duk dabi’u  kyawawa  na  addini kamar ,gaskiya ,hakuri, yakini akan abinda mutum yake yi ,kyauta da dabi’ar mutunta kai”muru’a”ya kuma bukaci mahalarta su yi dubi cikin lamurransu domin siffantuwa da irin wadannan dabi’u saboda da irinsu ne kawai za a iya kawo gyara a cikin al’umma..
A jawabin kammal  wannan taro da ya  gabatar,  Malam Yakubu Yahaya  ya fara ne da gode ma Allah (T) da ya hukumta yin wannan taro na ‘ya’yan Shahidai masu albarka  a wannan Gari na Katsina,sai ya bayyana Shahada da cewa, ita ce sirrin nasara ”bama addini ba har lamurran rayuwa  ana bukatar sadaukarwa inada ya nusar  ta hanyar kawo wasu misalan al’ummu da suka sadaukar domin  su kubutar da kansu daga danniyar ‘yan mulkin mallaka inda  ya bayar da misalin gwagwarmayar mutanen Kenya da Aljeriya  a yayin kwatar kansu daga Turawa,sannan ya ce. Gwargwadon  sadaukarwarmu, daidai nasara da zamu samu sai ya nuna muhimmancin mu kara sadaukarwa  akan wannan tafarki na Addini” yadda  tarbiyya ta gurbata a wannan al’umma tamu, mafita daga wannan yanayi yana bukatar sadaukarwa”. Malam Yakubu  ya ce, Allah ya yi mana baiwar kasha  99 bisa dari domin ya albarkace  mu da  jagoranci , kuma wannan jagoranci  shi ne  makami na nasar saura kashi  daya  ake bukatar mu aikata, wannan  kashi guda kuma  shi ne “ji da  bi” ga wannan jagora . Malam Yakubun ya jawo hankalin ‘ya’yan Shahidan  da  cewa, su tsayu akan abinda  iyayensu suka sadaukar da rayuwarsun akansa watau gwagwarmayar addini sannan su guji aikata duk abinda za ya bakanta ran mahaifansu domin suna kawo masu ziyara lokaci-lokaci kamar yadda ya tabbata a Hadisin Annabi(S) Ya kuma bukaci  masu kula da iyalan shahidan  da s kara u kula da abubuwan da  yaran  su kanyi , a kwabe su idan suka yi abin da bai kamata ba. Ya tsoratar da yaran cewa, su guji yi kahon cewa, su ‘ya’yan sahidai ne  amma  su basu yin aikin da iyayen nasu suka  yi,  inda  ya  ce wannan ba zaya  fitar da su ba a lahira  sai dai idan sun yi aiki na kwarai . ya  kuma ankarar akan al’amarin wayoyin yaran da cewa, akwai  bukatar a rika kulawa da halin da wayoyin yaran suke ciki, domin akwai makircin bata  tarbiyyar ‘ya’yanmu da aka bollo da shi ta hanyar wayoyin tafi da gidanka.
A wannan mu’tamar an  samu nasarar kai ziyarori a wuraren  tarihi  da suka hada da Hasumiyar Gobarau,da Makabartar Dan Marna  wani waliyyi da aka yi  a Katsina  sai zuwa rijiyar  Gusugu dake birnin Daura tare da ziyatar shahid Ibrahim Muhammad Zariya da ya sami shahadarsa a lokacin waki’ar  janar Abacha.
Manufar shirya wannan taro dai  kamar yadda  Malam Abdul Hamid ya bayyana ma almizan shi   ne gina tarbiyyar ‘ya’yan  shahidai  a tafarkin da iyayensu  suka sadaukar da rayukansu  tare da wayar masu da kawunansu akan muhimman wurare na tarihi dake cikin wannan kasa.