A ranar Laraba ne 25/ n2/ 1433 A.H,tawagar ‘yanuwa na Dandalin matasa na yankin Kano, suka kawo ziyara ga takwarorinsu da ke Katsina domin sada zumunci tare da gabatar da jawabai na karfafa juna.
A jawabin da ya gabatar , shugaban dandalin na matasan harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) Malam Hafizu Dauda Kano, ya ankarar da ‘yanuwa matasa na gwagwarmaya akan manufar wannan ziyara , inda yace,domi sada zumunci ne da tattauna yadda za a iya haduwa a karfafa juna , sai ya ce, akwai bukatar kowanensu ya kula da kansa ta hanyar siffatuwa da kyawawan dabi’u, ganin cewa a yanzu akwai gurbacewar tarbiyya. Ya kuma ya karfafi ‘yan dandalin da suci gaba da nemo malaman harka, ko masana su rika yi masu bayani akan wasu bangarori na harka, ya kuma yi kira ga Malaman harkar nan da kara sa kula su fahinci matsalolin matasan domin a shigowa da magancce su.
A wani sashen jawabin , Malam Hafizu ya tunanatar da ‘yanuwan cewa,Sayyid (H) ya bayyana matasa a maatsayin jari na wannan harka,sai ya nuna wajabcin siffantuwa da kyawawan ayyuka kamar yadda Sayyid din yake koyarwa, sannan ya bukaci matasan su kauce ma munanan ayyuka da za su jawo suka ga wannan kira da Sayyid din ke ma jagoranci. ya kuma bukaci matasa su kara kulawa da al’amurran harka ta hanyar nazartar tarihinn kiran, yaddad harkar ta taso da irin sadaukarwar da magabatanta suka yi domin samun damar tsayuwa akan ta.Sai yayi kira akan dagewa da ibada ta hanyar azumomi da sallolin na da makamantansu. A karshen jawabin nasa, ya bukaci kowane matashi ya zamo yana da wata gudunmuwa da yake bayarwa a wannan harka domin ta ci gaba.
A nasa jawabin, danuwa Sanusi Idris Musa, jawo hankalin matasa ya yi ta hanyar nuna takaicin yadda suke wahalar da maluman harka ta yin watsi da shiryarwar da suke yi a kodayaushe, sai ya bukaci matasan su sa tunani tare da nazartar maganganun Maluman, da kuma yin aiki da su.Ya ce koda kashi Hamsin cikin Dari na maganganunsu aka yi aiki da su, to da an ga sauyi a rayuwar matasan. Ya shawarci matasan da cewa, kowanensu ya duba ya ga inda yake da gajiyawa ya yi aiki domin gyara matsalarsa saboda ana yin wannan harka ne domin neman yardar Allah(T).
Malama Fatima Yusuf Ali , daya daga cikin wadanda suka kawo ziyarar daga Kano, ta bukaci ‘yanuwa maza da mata da su himmatu akan neman sanin ilmomi tare da sanin ilimin computer da harkar internet domin yada da’awar Malam (H),ta kuma jawo hankali akan dagewa dai da mujahada domin iya tunkarar halin da ake ciki a yanzu haka.
A jawabin godiya da ya gabatar, Shamsuddin Ahmad a madadin ‘yan dandalin na yankin Katsina, ya nuna godiya ga , maziyartan da wannan ziyara da suka kawo masu , ya kuma yi fatan su ‘yan kwamitin za su yi amfani da duk abubuwan da suka ji a wannan zama.
An kammala wannan ziyara cikin nasara, kuma tuni bakin suka isa gida lafiya.