Thursday, October 28, 2010

AN GABATAR DA WA'AZIN GORON SALLAH A ZANGON ALARAMMA


Daga: Abdul'Hamid Sani Ilya

Ranar Asabar 9 ga Shawwal, 1431 da yamma `yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Zangon Alaramma da ke kusa da garin Tsakatsa a Charanci jihar Katsina suka gabatar da Wa’azin goron Salla a garin Zango.
Wanda ya gabatar da Wa’azin a garin ga dimbin al’ummar Musulmin da suka taru don sauraren, shine Wakilin ‘Yanuwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Ganuwa, Rawayau da Kewaye,watau Malam Abdulhamid Iliya Ganuwa.
Malamin ya yi kira ga al’ummar Musulmi da cewa, “Lalle ya kamata mu tuna da makasudin abin da ya sa Allah Ya halicce mu, kuma Ya kawo mu wannan Duniyar da muke rayuwa a cikinta, wadda ko ba-dade ko ba-jima zuwa gare shi zamu koma ko mun so ko mun ki”.
Ya kara da cewa, “A she, in kuwa haka ne, ya zama wajibi a gare mu, musamman mu Musulmi, musan yadda zamu bautawa Allah Madaukkin Sarki ta hanyar bin dokokinsa wadanda ya aiko Manzonsa, Annabi Muhammadu (S) da su zuwa ga bayinsa don mu samu tsira  da kyakkyawan sakamako a wurin Allah ya yin da muka koma zuwa gare Shi a gobe Lahira.”
Sannan Malam Abdulhamid ya karanto ayar nan ta cikin AlKur’ani mai girma wadda Allah Ta’alah ke cewa, “Kuma ban halitta Aljannu da Mutane ba sai domin su bauta mani.” Sai Malam Abdulhamid ya ce, “Hakika wannan ayar ta na nuna mana makasudin abin da ya sa Allah Ta’alah Ya halicci Aljannu da Mutane.”
Kuma ya ci gaba da cewa, “Don haka ba wanda ya cancanci a bautamawa in ba Allah Madaukakin Sarki ba! Kuma wannan shine abin da Allah Ya ke ummurtarmu da shi  a waccan ayar ta Alkur’ani mai girma.
Malam Abdulhamid ya ci gaba da cewa, “In ko muna san musan yadda Allah Ta’alah Ke son a bauta masa, ya zama ba makawa gare mu dole sai mun komawa bin dokokin Allah Ta’alah kai tsaye in har muna son mu fassara waccan ayar da aikata ta a aikace yadda Allah (SWT) Ke so.”
Ya kara da cewa, “ Saboda haka wajibin mu ne mu bi koyarwar Manzon Allah, Annabi Muhammadu (S) da kuma koyarwar Iyalan gidansa tsarkaka, ma’asumai in har muna son musan yadda Allah Ta’alah ke son a bauta masa don mu samu tsira a Lahira! “Wannan kuma shine kiran da Maulana, Mujaddadi, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya kwashe sama da shekara talatin ya na yi wa bayin Allah da ke wannan nahiya bayani domin mu koma wa bin tsarin dokokin Allah (SWT) in har mu na son mu samu tsira daga azaba a gobe lahira.”

Malam Abdulhamid ya ce, “Godiya da yabo sun tabbata ga Allah Madaukkian Sarki da Ya fahimtar da mu wannan kiran na a komawa tsarin Allah da dokokinsa da Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ke yi a halin da ake ciki yanzu. Tare da fatar Allah Ya amfanar da mu abin da muka ji, Ya kuma ba mu ikon aikatawa.”